Yadda Takkadama Ta Kanannande Siyasar Kananan Hukumomi A Shekarar 2024
Manage episode 458314038 series 3311743
Zabukan Kananan hukumomi na cikin al’amuran da suka dauki hankali a fagen siyasar Najeriya a shekarar 2024.
Duk da an gudanar da zabukan cike gurbi a wasu daga cikin jihohin Najeriya, zabukan kananan hukumomi na cikin batutuwan da ’yan Najeriya suka fi zantawa a kai, mai yiwuwa saboda ganin da ake yi cewa wadannan zabukan sun fi shafar alumma kai tsaye.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi waiwaye a kan kurar da wasu daga cikin zabubbukan kananan hukumomi suka tayar a 2024
715 حلقات