Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.
Manage episode 450284013 series 3311743
A ranar Asabar 16 ga wannan watan ne za’a gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo, sai dai kamar sauran zabukan da aka saba gudanarwa a Najeriya, tuni masu ruwa da tsaki suka bayyana kammala shirye shiryen tunkarar wannan zabe.
To amma ba’a nan gizo ke sakar ba, domin kuwa a mafi yawan lokuta al’umma a kasar nan na korafin cewar duk da shirye shiryen da masu ruwa da tsaki suke bayyana kammalawa, a karshe ana samun matsala.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna da masu ruwa da tsaki ne kan yanayin shirye shirye don tunkarar zaben gwamna a jihar Ondo.
694 حلقات