Tasirin da salon koyarwa ke da shi wajen baiwa ɗalibai ingantatcen ilimi
Manage episode 454791882 series 1083810
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan mako, ya tattauna ne a kan salon koyarwa tun daga matakin makarantu na ƙasa wato ‘Method of Teaching’ a turance, da tasirin da wannan salo ke da shi kan bayar da ilimi. Salo ko kuma dabarun koyarwa matakai ne ko tsarin da malamai ke amfani da su wajen koyar da ɗalibai darussa, a kuma tabbatar da cewa ɗaliban sun fahimci darasin da ake yi musu.
A mafi yawan lokuta waɗannan dabaru sukan bambamta a tsakanin darussa, zalika ya danganta da matakan ilimi daga ƙasa, da na tsakiya zuwa na sama.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.......
23 حلقات