Yadda "Sojoji Suka Kashe Farar Hula" A Karo Na Biyu A Wata Guda
Manage episode 460895721 series 3311743
Bayanai na kara bayyana game da wani hari da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta kai a kan wasu kauyuka biyu na Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadin mutuwar farar hula akalla 15.
Wadanda suka shaida faruwar lamarin dai sun ce sojojin sun kai hari da jirgi mai saukar ungulu ne a kauyukan biyu wadanda ’yan bindiga suka kaiwa hari .
Wannan na zuwa ne makonni kusan uku bayan da Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kai wani harin irin wannan a Karamar Hukumar Silame dake jihar Sakkwato wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan abin da ya biyo bayan harin.
715 حلقات